15 Afirilu 2022 - 13:44
An Saki Sheikh Kazem Al-Omari Daga Gidan Yarin Saudiyya

Gwamnatin Saudiyya ta saki Hujjatul Walmuslimeen Kazem al-Omari, wanda ya kasance fitaccen dan shi'ar Madina ne.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo labarin cewa, gwamnatin Al-Saud ta sako Hujjatul-Islam wal-Muslimin Sheikh "Kazem al-Omari" daga gidan yari. Hujjatul-Islam wal-Muslimin Sheikh "Kazem al-Omari" wani jigo ne a cikin 'yan shi'ar Madina kuma dan marigayi Ayatullah Sheikh "Mohammad Ali al-Omari.

An kama shi a watan Fabrairun bara (2021); ba tare bayyana wani dalili ba!

Sheikh Kazem Al-Omari shi ne wakilin manya-manyan Marajio'in koyi a Madina kuma ba ya shiga wani yunkurorin siyasa. A lokacin rani na 2010, jami'an tsaron Saudiyya sun tsare shi na tsawon kwanaki 20 tare da mayar da shi wani wuri da ba a sani ba. Sakin nasa ya zo ne a daidai lokacin da wasu masu fada a ji na addini da na siyasa da kuma 'yan Shi'a daga garuruwa daban-daban na Saudiyya ke tattaunawa da jami'an gwamnatin Saudiyyar tare da neman a gaggauta sakin sa.

342/